Dan wasan Real Madrid kuma mai riƙe da kambun gwarzon ɗan kwallon kafan duniya, Luka Modric, ya ce har yanzu, ƴan wasan gaba na ƙungiyar sun kasa maye gurbin Cristiano Ronaldo tun da ya bar ƙungiyar.
Modric ya bayyana hakan ne, a lokacin da suke shirin fuskantar wasa dan ƙungiyar Ajax a jiya Talata, a gasar zakarun turai, inda za su karbi bakuncin kungiyar
Gwarzon ɗan wasan ya ce tun bayan rabuwa da Cristiano Ronaldo da ya koma Juventus, Real Madrid ta gaza ci gaba da nuna kwazo wajen zura ƙwallaye da kuma samun nasarori kamar yadda suke a baya.
A tsawon kusan shekaru 10 da Ronaldo ya shafe tare da Real Madrid, ya zura mata ƙwallaye 451, a wasanni 438 da ya buga mata. Sai dai bayan tafiyarsa Juvenus da kuma ajiye aiki da tsohon kocinsu Zinaden Zidane yayi, kungiyar ta soma fuskantar matsaloli.
A cewar Modric dole ne su samu wanda zai maye gurbin Ronaldo in ba haka ba kuwa dole a cigaba da rashin samun nasara a ƙungiyar.


