Connect with us

Labarin wasanni

Har yanzu bamu samu wanda zai maye gurbin Ronaldo ba shiyasa muke ta fuskantar matsala- MORDRIC

Published

on

Dan wasan Real Madrid kuma mai riƙe da kambun gwarzon ɗan kwallon kafan duniya, Luka Modric, ya ce har yanzu, ƴan wasan gaba na ƙungiyar sun kasa maye gurbin Cristiano Ronaldo tun da ya bar ƙungiyar.
Modric ya bayyana hakan ne, a lokacin da suke shirin fuskantar wasa dan ƙungiyar Ajax a jiya Talata, a gasar zakarun turai, inda za su karbi bakuncin kungiyar
Gwarzon ɗan wasan ya ce tun bayan rabuwa da Cristiano Ronaldo da ya koma Juventus, Real Madrid ta gaza ci gaba da nuna kwazo wajen zura ƙwallaye da kuma samun nasarori kamar yadda suke a baya.
A tsawon kusan shekaru 10 da Ronaldo ya shafe tare da Real Madrid, ya zura mata ƙwallaye 451, a wasanni 438 da ya buga mata. Sai dai bayan tafiyarsa Juvenus da kuma ajiye aiki da tsohon kocinsu Zinaden Zidane yayi, kungiyar ta soma fuskantar matsaloli.
A cewar Modric dole ne su samu wanda zai maye gurbin Ronaldo in ba haka ba kuwa dole a cigaba da rashin samun nasara a ƙungiyar.

Click to comment

Leave a Reply

Labarin wasanni

Kungiyar Kwallon Kafa Ta Manchester United Ta Cire Dan Wasanta Anthony Matial A Tawagar Da Za Ta Fafata Wasan Karshe Na Kofin FA

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta cire dan wasanta Anthony Matial a cikin tawagar da za ta fafata wasan karshe na kufin FA .

Kamar yadda kungiyar ta fitar a jiya Talata ta ce dan wasan Matial ya samu rauni don haka ba zai samu damar bugawa kungiyar wasa ba.

Dan wasan na Faransa wato Anthony Jordan Matial ya na da shekaru 27 sannan ya fafata wasanni kimanin 162 a Manchester United tare da cin kwallaye 62 tun bayan zuwansa Man United daga Manaco shekarar 2015.

Wasan Wanda ake saran fafatawa a ranar Asabar Wanda da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City shi ne wasan karshe don daukar kofin FA a kasar Birtaniya.

A makon da yagabata ne ranar Lahadi Man United ta doke Fulham da ci 2-1 a gasar.
Sannan ana saran fafatawar da Man City a ranar Asabar.

Continue Reading

Labarin wasanni

Ana Tuhumar Barcelona Da Laifin Bawa Alkalan Wasa Cin Hanci

Published

on

An tuhumi kungiyar kwallon kafa ta Barcelona dake kasar Sifaniya, bisa zargin bayar da cin hanci ga kungiyar alkalan wasanni, wanda Barcelonan ta musanta.

Ana tuhumar kungiyar ne dai da laifin na bayar da cin haci dangane da wani biyan kudi da suka yi ga Jos Maria Enriquez Negreira, wanda shine tsohon mataimakin shugaban kungiyar alkalan wasannin kasar Sifaniya.

A watan da ya gabata an gano cewa kungiyar ta bawa Negreira da kamfaninsa kudi kimanin Yuro Miliyan 8 da dubu 400, a tsakanin shekarar 2001 zuwa shekarar 2018.

A Juma’ar da ta gabata ne dai aka sanar da kotu a Birnin na Barcelona cewa, kungiyar da tsoffin shugabanni da Negreira ana zargin su da laifin rashawa, karya ka’ida da kuma harkar kasuwancin karya.

Hakan ya faru ne kwanaki Kadan da shugaban na Barcelona Joan Laporta ya karyata cewa, kungiyar tasu ta bawa alkalan Wasanni kudi.

Shugaban gasar Laliga JavierTebas a nasa bangaren yace, Laporta din ya kamata yayi murabus daga mukaminsa tunda ya kasa fito yayi bayanin yaddda musayar kudin ta kasance.

Tun farko dai wani gidan rediyo mai suna Ser Catalunya ne ya fara bayyana cewa, hukumar karbar haraji sun gudanar da bincike akan kamfanin Negreira Dasnil 95.

Continue Reading

Labarin wasanni

Ina Da Burin Taka Leda A Gasar Firimiyar Ingila – Osimhen

Published

on

Dan wasan da ke kan gaba wajen jefa kwallo a gasar Siriya A ta kasar Italiya Victor Osimhen yace, yana mafarkin taka leda a gasar firimiyar kasar Ingila.

Dan wasan gaban kasa Najeriyar wanda ya kasance a Birnin Rum dan karbar kyautar zakakurin dan wasa daga haure, yace yana son kawo Babbar gasa ga Kungiyarsa ta Napoli kuma yana son ya d’an gusa.

“Da yawan mutane suna ganin gasar firimiyar Ingila a matsayin babbar gasa mafi girma a Duniya.” Osimhen ya fada.

Kuma ya kara da cewa “yanzu ina cikin daya daga manyan gasoshi na Duniya, wato Siriya A ta Italiya.”

“Kwarai dagaske ina yin dukkan mai yiwuwa dan cimma buri na na bugawa a gasar Firimiya wata rana, amma komai zuwa yake kuma zan cigaba da kokari” in ji Osimhen.

Osimhen ya koma kungiyar Napoli ne a shekarar 2020, daga kungiyar Lille ta Faransa.

Yanzu haka ya jefa kwallaye 19 a wannan kakar wasannin, kuma kungiyar Napoli ita ke jan ragamar jadawalin gasar da tazarar maki 15.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: