Labaran jiha
Kotu ta kwace takarar me neman kujerar gwamnan Taraba a inuwar jam’iyar APC
Rahoton da mujallar matashiya take samu a yanzu haka, wata babbar kotun jihar Taraba ta dakatar da ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamna a jihar Taraba, kotun ta dakatar da ɗan takarar ne mai suna, Alhaji Sani Abubakar Ɗanladi daga tsayawa takarar bayan da aka yi zargin bayyana shekarun ƙarya a takardun da ya miƙawa hukumar zaɓe mai zaman kanta. Lamarin ya faru ne an saura kwanaki uku a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha.
Idan ba’a manta ba wata kotu ta bada irin wannan makamancin umarnin ƙwace takarar mai neman gwamnan kano a inuwar jam’iyar PDP Engr Abba kabir yusif, amma shi ana zargin an tafka kura kure a zaɓen fiɗɗa gwani (primary Election).
Labaran jiha
Sarkin Musulmi Ya Nada Gwamna Nasir Na Kebbi A Matsayin Gwarzon Daular Usmaniyya
Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na lll ya nada gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris a sarautar gwarzon daular Usmaniyya.
Wakilin Sarkin Musulmi kuma sarkin Argungun Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya mika takardar nadin ga gwamnan a gidan gwamnatin Jihar ta Kebbi a jiya Juma’a.
Alhaji Sa’ad ya nada gwamna Nasir ne a sarautar ta Gwarzon Daular Usmaniyya ne bisa gudummuwar da yake bayarwa na taimakon al’ummar kasar.
Sarkin Muslumin ya bayyana cewa sarautar gwarzon daular Usmaniyya ana bayar da ita ne ga dukkan wanda ya sadaukar da kansa wajen taimakon al’ummar Jiharsa da dama Kasarsa baki daya.
Sarkin na Argungu ya kara da cewa masarautar Sarkin Musulmi na sa ne da irin gudummawa taimako da kuma kyautatawar da gwamnan ya ke bayarwa a wajen inganta rayuwar al’umma.
Acewar Argungun Majalisar masarautar sarkin Musulmi za ta bayyana ranar da za ta nadawa gwamnan rawanin sarautar nan ba da dadewa ba.
A yayin karbar takardar nadin gwamna Nasir ya mika godiyarsa ga masarautar sarkin Musulmi bisa dacewar da ta gani ta nadashi a matsayin.
Sannan gwamna Nasir ya ce gwamnatinsa da mutanen Jihar za su samar da lokaci domin zuwa yin godiya fadar Sarkin Musulmin da ke Jihar Sokoto domin nuna farin cikinsu da nadin da aka yi masa.
Labaran jiha
Gwamnan Legas Ya Yiwa Fursunoni Afuwa
Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarni sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban na fadin jihar.
Kwamishinam shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.
Gwamna ya amince da sakin mazauna gidan gyaran halin ne bisa shawarwarin da majalisar duba yiwuwar yiwa fursunoni afuwa ta jihar.
Labaran jiha
Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano
Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.
Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.
Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.
Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.
Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.
Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.
-
Labarai10 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare6 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada6 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai6 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari6 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari