Tsohon mai horar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid Zinedine Zidane ya nuna ki amincewa da sake komawa ƙungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid don ci gaba da horar da ita kamar yadda tsohon shugaban ƙungiyar, Ramon Calderon ya bayyana.
Zidane ya shaida wa shugaban Real Madrid, wato Florentino Perez cewa, ba zai dawo kungiyar a yanzu ba bayan ya bukaci dawowarsa.
Sai dai ya nuna alamar watakila ya sake karbar aikin horarwa da ƙungiyar a cikin watan Yuni.

Real Madrid tana shirin yiwa ƙungiyar gagarumin gyara saboda yadda ta gamu da matsalolin rashin nasara a bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: