Gwamnan jihar Kano ya bayyana cewar a shirye yake don ganin an sulhuntasu da mai gidansa kuma amininsa Sanata Rabi u Musa Kwankwaso.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne cikin wata hira da ya yi a jiya.
Wakilin mujallar Matashiya ta rawaito gwamnan ya ce baya gaba da mai gidansa, kuma ya bayar da dukkan wata kafa don ganin an sulhuntasu amma abin bai yuwu ba.

A cewar Gwamnan Kano, har shugaban ƙasa da kansa ya nemi a sulhuntasu, amma a wannan ranar, ƙasa da awanni 24 Kwankwaso ya bayyana ficewarsa daga jam iyyar ta APC.

A dai dai lokacin da ake tinkarar ranar zaɓen gwamnoni da ƴan majalisu, gwamna Ganduje ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta ganin irin cigaban da ya kawo a zamanin mulkinsa.
Ana fargabar zaɓen gwamna a wasu jihohi ciki har da jihar Kano, ganin yadda dangantaka ta ƙara tsami tun bayan dawowa da ɗan takarar gwamna na jam iyyar PDP Abba kabir da aka fi sani da Abba Gida gida takararsa, bayan da wata kotu a jihar kano ta bayyana cireshi daga takara.
Sun ɗaukaka ƙara inda babbar kotu da ke Kaduna ta dawo masa da takararsa.