Tsananin tashin hankali na shiga yayin da na rabu da magoya bayana – Kwankwaso

Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Rabi u Kwankwaso ya bayyana cewar ba ya faɗa da kowa, kuma ko da ya ɓatawa wani zai iya dawowa don su shirya.
Sanata Kwankwaso dai ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi ta awanni biyu a kafafen yaɗa labarai na Kano, ya ce bai ji daɗin rabuwa da magoya bayansa ba, musamman waɗanda suke ganin bai kyauta musu ba.

“Duk wanda yake gani na ɓata masa zai iya dawowa don mu shirya” Inji Kwankwaso.

Cikin tattaunawa da ƴan jarida Kwankwaso ya bayyana cewar ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba sanadin rabuwa da magoya bayansa.
A cewar madugun kwankwasiyyar, dole ne sai an saɓa da mutane idan gangar siyasa ta kaɗa, amma hakan ba yana nufin an ɓata kwata kwata ba kenan.
A dai dai lokacin da ake dab da shiga zaɓen gwamnoni da ƴan majalisu, jihar kano dai siyasar ta ƙara tsami ganin yadda rikici ke tsakanin Sanata Rabi u Kwankwaso da kuma Gwamna Abdullahi Ganduje, sai dai kalaman nasu na nuni da cewar kowa ya saduda don dawowa a yi tafiya tare kamar yadda Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana.
Karanta a nan – https://matashiya.com/2019/03/08/a-shirye-nake-a-sulhuntamu-da-mai-gida-na-kwankwaso/