Connect with us

Labaran jiha

EFCC ta kama masu siyan ƙuri a, A Kano

Published

on

A cheɗiya uku mazaɓar gwagwarwa da ke ƙaramar hukumar Nassarawa hukumar yaƙi da masu yiwa ƙasa zagon ƙasa ta cafke wani da ake kyauta zaton tsohon kansila ne a daidai lokacin da suke siyan ƙuri un mutane.

majiyarmu ta Kamfanindillancin labarai na ƙasa NAN ta rawaito cewa ma aikaciyar hukumar EFCC ce ta kamashi dumu dumu yana siyar masu yin zaɓe, a lokacin da ake tsaka da kaɗa ƙuri a.

sai dai har yanzu ba a bayyana sunansa ba, inda hukumar ke cigaba da bincike a kan lamarin.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran jiha

Sarkin Musulmi Ya Nada Gwamna Nasir Na Kebbi A Matsayin Gwarzon Daular Usmaniyya

Published

on

Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na lll ya nada gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris a sarautar gwarzon daular Usmaniyya.

 

Wakilin Sarkin Musulmi kuma sarkin Argungun Alhaji Samaila Muhammed Mera ne ya mika takardar nadin ga gwamnan a gidan gwamnatin Jihar ta Kebbi a jiya Juma’a.

 

Alhaji Sa’ad ya nada gwamna Nasir ne a sarautar ta Gwarzon Daular Usmaniyya ne bisa gudummuwar da yake bayarwa na taimakon al’ummar kasar.

 

Sarkin Muslumin ya bayyana cewa sarautar gwarzon daular Usmaniyya ana bayar da ita ne ga dukkan wanda ya sadaukar da kansa wajen taimakon al’ummar Jiharsa da dama Kasarsa baki daya.

 

Sarkin na Argungu ya kara da cewa masarautar Sarkin Musulmi na sa ne da irin gudummawa taimako da kuma kyautatawar da gwamnan ya ke bayarwa a wajen inganta rayuwar al’umma.

 

Acewar Argungun Majalisar masarautar sarkin Musulmi za ta bayyana ranar da za ta nadawa gwamnan rawanin sarautar nan ba da dadewa ba.

 

A yayin karbar takardar nadin gwamna Nasir ya mika godiyarsa ga masarautar sarkin Musulmi bisa dacewar da ta gani ta nadashi a matsayin.

 

Sannan gwamna Nasir ya ce gwamnatinsa da mutanen Jihar za su samar da lokaci domin zuwa yin godiya fadar Sarkin Musulmin da ke Jihar Sokoto domin nuna farin cikinsu da nadin da aka yi masa.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnan Legas Ya Yiwa Fursunoni Afuwa

Published

on

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayar da umarni sakin fursunoni 55 daga gidajen gyaran hali daban-daban na fadin jihar.

Kwamishinam shari’a na jihar, Lawal Pedro, SAN, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu.

Gwamna ya amince da sakin mazauna gidan gyaran halin ne bisa shawarwarin da majalisar duba yiwuwar yiwa fursunoni afuwa ta jihar.

Continue Reading

Labaran jiha

Babu Batun Rikici Tsakanin Kwankwaso Da Abba – Gwamnatin Kano

Published

on

Wasu rahotannin na nuni da cewa, bayan ci gaba da fuskantar rikice-riciken cikin gida da ake ci gaba da fuskanta a jam’iyyar NNPP a Kano, gwamnan Jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya daina daga Wayar uban gidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Rahotanni sun bayyana cewa daga cikin abubuwa da suka kara rura wutar rikicin jam’iyyar ciki harda batun nada Kwamishinoni.

Hakan ya sanya gwamna Abba Kabir ya gujewa haduwa da jagoran nasa Rabi u Kwankwaso.

Sai dai bayan bullar takun sakar da ya fara shiga tsakanin Kwankwaso da Abba, gwamnatin Jihar ta Kano ta fito ta musantan jita-jitar da ke yawo cewa baraka ta kunno kai tsakanin gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf da ubangidansa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, har ta kai ga baya daga wayarsa.

Hadimin gwamnan na musamman kan shafukan sada zumunta Salisu Yahya Hotoro ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da yayi a shafinsa na facebook a yau Litinin.

Hadimin gwamnan ya bayyana cewa ko kadan babu kanshin gaskiya a cikin rahotannin da ake yadawa akan Kwakwaso da Abba.

Acewar Hotoro har yanzu akwai alaka mai karfi tsakanin Kwankwaso da Abba, babu wani abu da ta shiga tsakaninsu.

Gwamnatin ta Kano ta bukaci mutane da su yi watsi da jita-jitar da ba ta da tushe balle makama.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: