A unguwanni da dama musamman yankin bachirawa, kurna da miltara, matasa da yawa suna wasanni da ababen hawa don nuna murnar zaɓen gwaninsu Abba Kabir da akafi sani da Abba Gida Gida na jam iyyar PDP.

Tawagar mujallar Matashiya ta kwaci kanta da kyar bayan da matasan suka tare gaban motar da suke tafiya a dai dai lokacin da suke tsaka da nuna murnarsu.
A yau ne aka gudanar da zaɓen gwamna da ,yan majalisu wanda ake sa ra fara kawo sakamako kowanne lokaci daga yanzu.

