Sakamakon rashin bayyanar sakamakon zaben gwamna na karamar Hukumar Nasarawa a gaban Babban jami’in tattara sakamakon zaben a nan kano Farfesa R.A Shehu yace An dage cigaba da zaman tattara sakamokon har sai an gano sakamakon zaben Karamar Hukumar Nasarawa.

Farfesa R.A Shehu yace sun samin labarin an yaga sakamakon zaben na Nasarawa don haka yace ya zamar musu Dole su dage zaman zuwa wani lokaci da bai bayyana ba.

Yanzu haka dai jami’in tattara sakamakon ya karbi sakamakon kananan Hukumomi guda 43 cikin 44.

Da yake ta’aliki kan matsalar da aka samu kwamishinan Hukumar zabe na kano Farfesa Riskuwa Arahu Shehu yace zabu dubu wuraren da aka soke zabensu ta fuskar dokar zabe,idan sun yi dai-dai da doka to za’a sake zabe a wuraren .

Wakilin mujallar Matashiya Yakubu Abubakar Gwagwarwa ya bamu labarin cewa an samar da tsaro Mai tarin yawa a of


fishin Hukumar zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: