Hukumar zaɓe mai zaman kanta INEC reshen jihar Kano ta bayyana cewa duba ga adadin mazaɓun da aka soke za su iya sauya alƙaluman ne ya sa tilas a sake gudanar da zaɓe a mazaɓun ƙasa da kwanaki 21 kamar yadda dokar hukumar zaɓen ta tanada.

Fafesa B.B Shehu ne ya bayyana hakan bayan tattara alƙaluman zaɓen da aka gabatar a hukumar zaɓen ta jihar Kano.

Sai dai dubban magoya bayan wanda ke kan gaba a yawan ƙuri;u sun fito suna nuna murnarsu a ciki da wajen jihar Kano.

Ko da yake a jiya ma magoya bayan gwamnan mai ci sun nuna nasu farin cikin a dai dai lokacin da gwamnan ke kan gaba a yawan ƙuri;u.
Ana sa ran gudanar da kwantan zaɓen a ƙasa da kwanaki 21.