Gwamnatin Aljeriya ta ɗauki matakin rufe ilahirin jami’o’in ƙasar, makwanni biyu kafin fara hutunsu a hukumance, don daƙile aniyar dubban ɗaliban da ke shiga zanga-zangar adawa da tazarcen shugaba AbdelAziz Bouteflika, da yake yunƙurin yi.
Dubban jama’a dai na ci gaba da yin dandazo a birnin Algiers, tattare da aniyar tilasta kawo ƙarshen shugabancin Bouteflika na tsawon shekaru 20, da a yanzu ke neman wa’adi na biyu.
A wani Rahoton da mujallar matashiya ta samu na nuni da cewa jami’an tsaron ƙasar sun kame aƙalla masu zanga-zanga 195, da aikata laifukan fasa shaguna, da kuma tayar da hatsaniya.
A halin da ake ciki, sama da makwanni biyu ke nan shugaban na Aljeriya yana ƙasar Switzerland inda ake duba lafiyarsa.
Tun a shekarar 2013, Bouteflika ya daina fita cikin jama’a bayan kamuwa da ciwon mutuwar barin jiki.
Amma sai yau ya dawo ƙasar har kuma jami’an tsaro suka yi masa jerin gwanon taya shi murnar dawowa ƙasar sa.


