Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da dawowar tsohon mai horar da ƙungiyar ta,Zinadine Zidane horar da ƴan wasanta.
Tun bayan dakatar da Santiago Solari daga horar da ƴan wasan ajin farko zuwa horar da ƴan wasan Club din masu tasowa. Zidane ya ajiye aikinsa ne da kansa inda ya sanar da murabus dinsa bayan ya lashe kofuna. Zidane ya ajiye aikine kwanaki 2 bayan kai Club din ga nasarar cin kofin zakarun Turai karo na 3 a jere.
Tuni dai Real Madrid ta sanar da matakin bai wa Zidane sabon kwantiragin shekaru 3 wanda zai kai shi nan da shekarar 2022.
Yanzu haka dai Real Madrid na matsayin na 3 ne a teburin Laliga da tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona da ke saman tebur.


