Daga Abubakar Murtala Ibrahim

Hukumar zaɓe ta ƙasa Inec reshen jihar Kano ta bayyana cewar, kundin dokokin hukumar ne ya bata damar ɗage faɗar sakamakon zaɓen da ya gudana a ranar 9 ga watan Maris ɗin da muke ciki.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannun kwamishinan zaɓe na hukumar, Farfesa Riskuwa Arabu Shehu kuma aka aikewa mujallar Matashiya, ya ce, hukumar ta yi dogaro da sashe na 41 (e)  wanda sashen ya ce ” DUK ZAƁEN DA YA GUDANA AKA SAMU ADADIN ƘURI U MASU RINJAYEN DA ZA SU IYA SAUYA ALƘALUMA, WAJIBI NE A KOMA MAZAƁUN A GUDANAR DA ZAƁE KAFIN SANAR DA SAKAMAKO, HAKA KUMA ZA A GUDANAR DA ZAƁE A DUKKAN WURAREN DA AKA SOKE, DA WANDA AKA SAMU RIKICI DA MA INDA AKA SAMU YAWAN ƘURI U FIYE DA ADADIN MUTANEN DA AKA TANTANCE”

Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya ce, a zaɓen da ya gudana akwai wuraren da aka samu yawan ƙuri u fiye da mutanen da aka tantance, kuma jimillar ƙuri un da aka soke da wuraren da aka samu matsala sun kai 128,572, kuma ƙuri un da ke fifiko tsakanin jam iyyun da suka samu mafi rinjayen ƙuri u 26,655.

An samu wannan matsaloli a akwatuna 210, cikin mazaɓu 88 da ke ciki da ƙauyukan jihar Kano.

Wannan dalili ne ya sa wajibi aka saka ranar 23 ga watan maris don sake zaɓe a mazaɓun suka tsinci kansu cikin wannan matsala.

Jam iyyar APC ta samu yawan ƙuri u 987,819

Yayin da PDP ta samu yawan ƙuri u 1,014,474.

Za a sake zaɓen ne a dukkan mazaɓun da aka samu matsala a ranar 23/03/2019.

Hukumar zaɓe INEC ta roƙi al umma da su bada haɗin kai don ganin an gudanar da sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: