Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta na Ƙasa INEC farfesa Mahmud yakubu, ya bayyana cewa babban aikin dake gaban ƴan majalisu a halin yanzu shi ne gyaran kundin tsarin zaɓe.
Farfesa ya bayyana hakan ne A lokacin da yake miƙa wa Ƴan majalisar dattijai shaidar zama zaɓɓaɓen ƴan majalisun da aka zaɓa a wannan zaɓe na shekarar 2019.
Farfesa ya ƙara da cewa kundin tsarin zaɓe na buƙatar sauye sauye wanda zai yi dai dai da zamani, kasancewar komai na buƙatar chanji hakan zai nuna lallai ƙasar mu ta ɗauko hanyar cigaba a fannin demokaraɗiya.
Idan ba’a manta majalisa ta miƙawa shugaban ƙasa kundin tsarin zaɓe don ya sa hannu akan wasu gyare gyare da sukayi.
Shugaba muhammad Buhari yaƙi sanya hannu inda ya ce an kawo masa kundin a dai dai lokacin da ake tunkarar zaɓe na 2019.