Prime ministan Ƙasar NewZealand Jacinda Ardern ta tabbatar da cewa Brenton Harrison ya tura mata saƙon zai kai hari a wasu masallatai.
Sai dai rashin sanin taka maimai wurin da za’a kai harin shi ya hana ɗaukar matakin gaggawa, duk da ya sanar da ita a ƙurarren lokaci tare da kai harin.
Harrison ɗan shekara 28 ya kai harin ne wani masallaci mai suna Alnoor inda ya harbe musulmai da yawansu ya kai 50, 34 kuma aka garzaya dasu asibiti, inda 12 a cikinsu suke cikin mawuyacin hali.
Yanzu haka dai Brenton Harrison yana tsare a hannun jami’an tsaro inda yake fuskantar tuhuma a kotu.


