Wata Kotun ladabtar da masana’antu ICN ta ƙasa ta zartar da hukuncin korar wasu jami’an ƴan sanda 3 da daga aiki,bisa kamasu da akayi same da laifin karbar cin hancin har kudi, dalar Amurka 5,000, ƴan sandan da aka kora sun haɗa da Joseph Okan,Joshua Madami masu muƙamin inspecto, sai Cyprian Nwanko mai muƙamin sajant, dukkansu an kama su da laifukan rashin ɗa’a da karbar cin hanci. Korarrun jami’an uku sun shigar da ƙara ne gaban kotun, inda suke ƙalubalantar matakin da babban sufeto-janar na ƴan sandan Najeriya ya ɗauka na sallamar su a aikin bayan an same su da laifukkan rashin ɗa’a da cin hanci da rashawa.
Mai shari’a Rakiya ta bayyana cewa masu shigar da ƙarar sun ƙalubalanci matakin da rundunar ƴan sandan Najeriya ta ɗauka, na sallamarsu daga aiki, suka yi zargin ba a bi dokokin rundunar ba wajen basu takardun sallamarsu daga aiki. Mai shari’a ta bayyana cewa mutanen uku basu da wata gamsasshiyar hujja da zasu gabatarwa a gaban kotun, sannan laifin da suka aikata sun saɓa da dokokin ɗaukar ma’aikata da rundunar ta nuna musu kafin ɗaukar su a aiki, don haka ba wata hujja da ta nuna cewa rundunar ƴan sandan ba ta bi ka’ida ba wajen Ɗaukar matakin korar.
Wannan dai shine matakin da shugaba muhammad Buhari yake ƙoƙarin yaƙar cin hanci da rashawa a ƙasa gaba daƴa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: