Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa, maimakon a fito da kuɗi a ranar zaɓen da za’a gudanar na cike gurbi a rabawa al’ummar mazaɓar Gama, don su zabe shi, to gwanda yayi mu su ayyukan raya ƙasa ko da kuwa ba shine zai lashe zaben ba,saboda za su daɗe su na ganin aikin kuma su na amfana da shi.
Gwamnan Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya je duba ayyukan da ake gudanar wa a mazabar Gama, wacce ita ce mazaɓa mafi girma da za a gudanar da zaɓen cike gurbi a ranar Asabar, 23 ga Maris, 2019.
Ganduje ya ƙara da cewa “Mu na yin wannan aiki ne tsakanin mu da Allah, Ba dan siyasa ba dama can aiki muke yi a jihar kano ba aika aika ba,Allah ne zai biya mu. Saboda haka ba magana ce ta riya ba.
Idan ba’a manta ba tun ranar da aka ayyana za’a sake zaben mazaɓar Gama suka samu tagomashin aikin titi daga hannun gwamntain jihar kano, wanda ake alaƙanta hakan da neman ƙuri’ar mazauna yankin Gama.

Leave a Reply

%d bloggers like this: