Ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Manchester United Paul Pogba ya bayyana Real Madrid a matsayin ƙungiyar da kowanne ɗan wasa yake d burin zuwa ƙungiyar, amma kuma ya ce shi a yanzu yana jin daɗin zamansa a Manchester United.
Ɗan wasan na tsakiya mai shekaru 26 ya yaba wa mai horar da ƙungiyar na riƙon-kwarya OleGunnar Solskjaer, sai dai yace Real Madrid ƙungiya ce wadda duk wani ɗan wasa zai so ya ganshi acan.
Pogba ya bayyana hakan A wani taron manema labarai a Faransa Pogba ya ce: Real Madrid na ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin ƙwallon kafa na duniya. A ko da yaushe ina faɗin cewa Real Madrid ƙungiya ce da kowa ne dan wasa ke fatan taka wa leda.” Inji shi.
Sai dai an masa tambaya kan yadda yake yabon ƙungiyar ko yana son sauya sheƙa ne zuwa can ?, sai ya ce; ”A yanzu dai ina farin cikin kasancewa a Manchester. Ina wasa. Ga kuma sabon koci, mai hazaƙa da iya tafiyar d ƴan wasa yadda y kamata.


