
Ɗan takarar Gwamna na Jam’iyar PRP wato Mallam Salihu Sagir Takai ya umarci magoya bayan sa da su zabi Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR na Jam’iyar APC a zaben karashe na gwamna da zaa gudanar ranar asabar mai zuwa.
Mallam Takai ya sanar da haka ne yayin da yake ganawa da magoya bayan sa a jiya. Ya shaida musu cewa Gwamna Ganduje ya neme shi sun tattauna kuma sun cimma matsaya, a cewarsa wannan shi ne zai zamto alheri ga jihar Kano. Kuma ya kara da cewa akwai kyakyawar alaka mai karfi tsakanin sa da Ganduje.

Don haka yake kira ga magoya bayan sa na Jam’iyar PRP da su fito kwansu da kwarkwata domin su kadɗawa Gwamna Ganduje kuri’un su a ranar asabar mai zuwa, 23 ga watan nan.
Mallam Salihu Takai ya samu kuri’u kimanin dubu dari 100,000.
