Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Mohammed Wakili ya bayyana cewa darajar ran dan Adam ta zama “kamar ta sauro”.

“Don sauro ne za a kashe shi ba za a ji komai ba” a cewarsa. Kuma ya ce wannan shi ne abin da ya fi firgita shi a aikinsa.

Kwamishinan ya bayyana haka ne a wata ta musamman da ya yi da BBC a shafinsu na facebook ranar Alhamis.

Ya ce duk kashe-kashen da ake yawan yi a Najeriya yanzu yana da nasaba da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Har ila yau, Kwamishinan ya ce ba ya goyon bayan ko wani bangare na siyasa, inda ya ce aikinsa amana ne kuma aiki ne na kare rayukan jama’a gaba daya.

“Idan na bi bayan daya, na zama azzalumi,” kamar yadda ya ce.

Ya ci gaba da cewa “Don me zan bi bayan jam’iyya daya, in ki daya? Bayan an ce ga yadda aikina yake, an ce kowa nawa ne.

“Abin kawai da zan yi shi ne in kare doka, in kare oda in kare dukiyoyin jama’a in kare rayukan jama’a – ba dan siyasa da wanda ba dan siyaasa ba. Har barawo ma aikina ya tanadi in kare shi.”

Daga nan, CP Wakili ya yi tsokaci kan dangantakarsa da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje inda ya ce akwai kyakkayawar alaka a tsakaninsu.

“In aiki ya taso yana nema na mu yi shawara kuma yana ba ni goyon baya 100 bisa 100”.

A makon da aka gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi ne dai ‘yan sanda a jihar Kanon suka kama mataimakin gwamnan jihar Nasiru Gawuna bisa zarginsa da yunkurin tafka magudin zabe.

Amma mataimakin gwamnan ya musanta zargin.

Hakazalika a wata tattaunawa da BBC ta yi da shi a baya, ya ce ana bincike ne kan sa hannun mataimakin a yaga sakamakon zaben karamar hukumar Nasarawa, inda ya ce za a dauki matakin da ya dace a kansa.

Har ila yau, a wata hirar da BBC a ranar Alhamis, Gwamna Ganduje ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda CP Wakili yake tafiyar da aikinsa a jihar.

Kwamishina Wakili ya bayyana cewa yana daf da yin ritaya a watan Mayun shekarar 2019.

A karshe ya ce shirye yake ya karbi duk wani mukami idan gwamnati ta yi sha’awar ba shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: