Kamar yadda hukumar zaɓe ta ayyana yau Asabar 23, ga watan Maris, 2019, Hukumar ta tsara kammala zaɓen wasu jihohi guda 18 waɗanda ta soke wasu mazaɓun kan wasu dalilan ta ta bayyana na basu kammala ba, a jihohi 18 daga cikin 36 da ke faɗin tarayyar Nijeriya.
Jihohin da hukumar INEC ta ayyana cewa zaɓukan su basu kammala ba.
Sun haɗa da Sakkwato da Filato da Benuwai da Kano da Adamawa da Bauchi, a likaci guda kuma aka rushe na jihar Ribers.
Daga bisani Hukumar INEC ta sake ɗaukar matsaya wajen gudanar da kammala zaɓen a jihar Kano da Sakkwato da Filato da Benuwai, tare da dakatar da gudanar da maimaita na Bauchi da Adamawa tun bayan da wata kotu ta bada Umarnin hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: