Jam’iyyar PDP a jihar Kano ta bukaci Hukumar Zabe INEC da ta soke karashen zaben gwamnan Kano da ke gudana a yau asabar a wasu sassa na jihar Kano.

Shugaban riko na jam’iyyar a nan Kano Rabi’u Sulaiman Bichi ne ya bukaci hakan yayin wani taron manema labarai da ya kirawo a nan Kano.
Rabi’u Sulaiman yace abun da ake gudanarwa a Kano ba zabe bane, inda ya zargi cewa ana gudanar da zaben ba ta hanyar da ta dace ba.

Shugaban jam’iyyar ta PDP yace suna nan suna duba irin matakin da ya dace su dauka kafin ace an bayyana Wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

kamar yadda rahotonanni kee nunawa a wasu wuraren an samu ɓullar baƙin ƴan sara suka da ke tayar da hankula a wasu mazaɓun.