Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya bayyana cewa, sai sun karɓi sakamako daga jami an tsaro kafin bayyana sakamako, ganin yaddaake ƙorafin an samu tashin hankali a wurare da dama.

Shugaban hukumar zaɓen ya bayyana cewar akwai ƙa ida da dokoki da hukumar ta samar kafin faɗar sakamako, sannan kuma kowa yana da damar yin ƙorafinsa a rubuce.

