Wani binciken masana a ƙasar Amurka ya nuna cewar akwai sinadarai da ke ƙara ƙarfin kwakwalwa waɗanda ke cikin kwai.

Binciken masana a kan bin diddigin kan sinadaran da ke ƙunshe cikin kwai ya nuna cewa matuƙar mutum na cin kwai aƙalla guda uku kullum na iya kaucewa da kamuwa da gigin tsufa.

Binciken wanda sashen bin diddigin ya tabbatar da cewa hatta mata masu ciki na buƙatar suna cin kwai wanda zai rage musu yawan laulayi da kuma ƙarawa jaririn da ke cikinsu lafiya

Haka kuma suka ce kwai na ɗauke da sinadarin Cholesteral wanda yake yaƙar cutar maiƙon jinin jikin ɗan adam.
Jami ar Oxford da ke ƙasar UK ta shirya samar da hanyoyin wayar da kai don ganin an buƙasa yadda za a samar da kwai a kullum.
Wani masani a jihar Kano Alhaji Muhammad Aminu Adamu ya bayyana cewar a sgekara ana samawa duk ɗan Najeriya ɗaya kwai 30, wanda ya ce hakan yayi ƙaranci akwai buƙatar a ƙara fiye da haka
Muhammad Aminu wanda shi ne shugaban gidan gonar Nana Farm ya bayyanawa mujallar Mataahiya cewar, saboda muhimmancin kwai a jikin ɗan adam ne ya sa majalisar ɗinkin duniya ta ware duk ranar 14 da 15 ga watan Oktobar kowacce shekara don bincike tare da sanar da duniya muhimmancin kwai