Bayanin dake fitowa ta bakin shugaban
Gwamnatin ƙasar Austria, Sebastian Kurz ya bayyana cewa, maharin masallacin Newzealand ya na da alaƙa da wata ƙungiya dake Rajin nuna wariyar Farar Fatar ta Austriliya.
Bayanai sun nuna cewa shugaban kungiyar, Martin Sellner ya karbi Euro dubu 1 da 500 a matsayin tallafi daga hannun wani mutun da sunansa ya yi daidai da na maharin na Masallatan birnin Christchurch a ƙasar New Zealand.
Kamar yadda mai magana da yawun masu shigar da ƙara ya bayyana.
Shima Shugaban ƙungiyar Masu Rajin Fifita Farar Fatar, ya tabbatar da cewa ya karɓi tallafin kuɗin a shekarar 2018,
Ya bayyana hakan ne a hoton bidiyo da ya wallafa YouTube, in da yake cewa tabbas, ya karbi kudin tallafi ɗauke da saƙon email da ke tattare da suna irin na wannan maharin.
Sai dai Sellner yace a shirye yake da ya miƙa kuɗaɗen a gidauniyar Agaji.
Jami’an ƴan sandan ƙasar NewZealand na cigaba da binciken wannan maharin da ya kashe musulmai 50 a masallaci don gano musabbabin kai wannan harin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: