Shugaban jam iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas ya bayyanawa mujallar Matashiya cewar, basu da labarin wata jam iyya ta kaisu ƙara kotu bisa ƙalubalantar zaɓe, idan ma hakan ta kasance a shiye suke don bayyana a gaban kotu.

Abdullahi Abbas ya bayyana hakan ne yayin wata gajeriyar tattaunawa da mujallar Matashiya.

Ya ce suna godiya bisa al umma da suka fito suka gudanar da zaɓe, a cewarsa, babu wani tashin hankali da ya auku a yayin zaɓen gwamna a jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: