Buba Marwa shine Shugaban kwamitin da shugaban ƙasa muhammad Buhari ya kafa da zai yi, yaƙi da shan miyagun kwayoyi, a Da yake jawabi kan wani ƙi yasi da aka fitar Alhaji Buba Marwa, ya bayyana cewa, ƙiyasin da aka yi na yawan ƴan Najeriya da suka kai Miliyan 180, bincike ya nuna cewa mutum miliyan 15 daga cikinsu duk ƴan kwaya ne.
Buba Marwa, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Legas a lokacin Soja ya ce, wannnan lamarin wani abin tayar da hankali ne, kasancewar ƙididdigar da ƙungiyoyin duniya suka yi, ya nuna cewa, in aka samu kashi 15 na mutanen dake ta’ammali da kwayoyi a ƙasa, to abin ya munana,

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta samar da wannan kwamitin ne don fito da hanyoyin maganin matsalar shan miyagun kwayoyi a faɗin ƙasar nan.
Kamar yadda shugaba muhammad Buhari ya ɗaura ɗambar yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasa baki ɗaya.

