Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Arsenal tayi nasarar siyan ɗan wasan baya dake ƙungiyar Bayern Munchen David Alaba dake ƙasar Jamus.
Tun a baya da ma ƙungiyar Munich ta bayyana cewa ɗan wasan zai iya barin ƙungiyar a ƙarshen kakar wasan bana. Alaba dai ya buga wasanni 24 a wannan kakar a wasannin Bundel Liga ya zura kwallaye 2 sannan kuma ya taimaka an zura kwallaye 2 wanda hakan yasa ƙungiyar take ganin baya ƙoƙari kamar shekarun baya.
Tuni dai ƙungiyar Arsenal ta siyi Alaba, a yayin da Munich ta maye gurbinsa da Lucas Hernandez daga ƙungiyar kwallon ƙafa Ta Atlentico Madrid dake ƙasar Spain.
Alaba, mai shekaru 26 a kwanakin baya ya taɓa bayyana cewa zai iya komawa ƙungiyar kwallon kafa ta Arsenal saboda tun yana yaro yake goyon bayan ƙungiyar.
A ɓangare guda kuma ƙungiyar kwallon kafa ta Manchester City ma tana zawarcinsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: