Kwamishin zaɓe a Jihar Kano Farfesa Riskuwa Arabu Shehu ya ce akwai buƙatar ilimi na musamman a ganin yadda za a wayar da kan mutane dangane da dokokin da suka shafi hukunar zaɓe mai zaman kanta.

Farfesa Riskuwa ya bayyana haƙan ne a yayin bayar da shaidar cin zaɓen ƴan siyasar da suka samu nasara a zaɓen 2019.
Mujallar Marashiya ta jiyo farfesa Riskuwa Arabu na cewa, da yawan mutane na yankewa hukumar hukunci ba tare da sanin cewa suma suna da iyaka ba, sannan kuma suna da dokoki da basu isa su ƙetara ba tunda suma suna ƙarƙashin doka.

” Ya kamata fannin kula da harkokin ilimi su faɗaɗa hanyoyin wayar da kan mutane bisa rashin fahimtar dokokin hukumar zaɓe, don babu wani abu da hukumar zaɓe ta isa ta yi na son rai illa abinda doka ta bata dama” Riskuwa.

Sannan ya shawarci ƴan takarar da suka samu nasara da su yi riƙo na amana sannan su tabbata sun saka tsoron Allah a mulkinsu ganin yadda babu wani da ake samun nasara ba tare da tsoron Allah ba.