Za a fara bada horon ɗaukar hoto ga matasa 100, ga duk mai sha awa zai iya ziyartar ofishin nujallar da ke lamba 1B france road a Kano.

A cewar shugaban mujallar Alhaji Abubakar Murtala Ibrahim ya ce, za su cigaba da bada horon sana o i daban daban ga matasa kuma kyauta.
Sai dai wannan karon ya bambanta da wanda aka yi a baya, ya ce an sabunta hanyoyin koyon sana o in cikin sauƙi kuma ba tare da an ɗauki kwanaki masu tsawo ba ta yadda matasa za su amfana.

Abubakar ya ce, a baya sun horas da matasafoye da 500 sana a kyauta, daga baya suka saka wani kuɗi da za a ringa biya, bayan nazari da ya yi ya fahimci da yawan matasan na son koyon sana ar amma ba su da halin yi ya sa suka soke kuɗin kuma za a gigaba da koyarwar kamar yadɗa aka kyauta.

Sai dai wani ƙalubale da ya ce zai iya kawo cikas don ganin an samawa matasan madogara bai wuce rashin samun jari ga matasan da aka horas ba.
Tsarin koyarwar a wannan lokaci zai ɗauki salon sana o i daban daban, kuma za a ke binsu daki daki har sai matasan sun fahimta kafin a kai ga basu takardar shaidar koyo daga Matashiya.
Abubakar ya yi kira ga duk wanda yake da dama kuma yake da sha awar sa hannu don kawar da zaman kashe wando a faɗin jihar da ma ƙasa baki ɗaya, da su duka hanyar da za su iya bada gudunmawarsu don ciyar da al umma gaba.