Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, tilas ne jam’iyyar PDP ta kori munafukai da masu yi mata zagon ƙasa a cikin mambobinta shine hanyar da zai dawo da martabarta, a idon ƴan Najeriya.
Obasanjo ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar PDP da su yi zawarcin wasu mutane ƙima da m muhimmanci wanda za su bayar da gudunmawa duk wuya duk runtsi”.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin wata tawagar shugabannin PDP daga yankin Kudu maso Yammacin Najeriya, wanda suka kawo mishi ziyara a gidansa da ya gina wanda yake ɗauke da katafaren ɗakin karatunsa da ke birnin Abeokuta na jihar Ogun.

A cewar Rfi hausa Obasanjo ya ce, da dama daga cikin shugabannin na PDP na cika aljihunsu da tumbinsu ne kawai, ya kuma ce, gurɓatattun mambobinta ba su da jajircewar da zasu iya dawo da martabar da jam’iyar ta rasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: