Hukumar Hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA Reshen jihar kano ta bayyana cewa a yanzu an samu raguwar shaye shaye a jihar kano daga kaso 3% zuwa kaso 1%.
Kwamandan hukumar ne na reshen jihar kano Dr Ibrahim Abdul ne ya bayyana hakan, a yau juma’a, lokacin da kwamitin dake ba da shawara ga shugaban ƙasa kan hanyoyin da za’a daƙile shaye shaye a faɗin Najeriya.
Dr Abdul ya jaddada hakan ne a gaban Shugaban ƙaramar hukumar fagge Alhaji Shehu Abdullahi kan yadda aka samu raguwar ƴan shaye shaye a jihar kano musamman yadda aka samu jajirtaccen kwamishinan ƴan sanda a jiha kano da yake yaƙi da ƴan ƙwaya.