Daga Abba Anwar

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewar sabuwar gwamnatinsa da za ta fara daga 29 ga Watan Mayu, 2019, za ta yi tafiya da matasa wajen gudanar da gwamnati. Bisa la’akari da irin gudummawar da matasan suke bayarwa wajen cigaban kasa.

Ya ce ya tabbatar matasan wannan jiha ba abinda yake gabansu illa ganin an samu cigaba mai dorewa a wannan jiha. Ya ce saboda haka “Ina yi musu albishir da cewa wannan sabuwar gwamnati mai shigowa za ta tafi da su ka’in da na’in.”

Gwamnan ya yi wannan albishir ne lokacin da shugabannin Majalisar Matasa Ta Kasa, wato “National Youth Council of Nigeria” karkashin jagorancin shugabansu na kasa, Bello Bala Shagari, ta kai masa ziyarar taya murnar sake samun nasarar zama gwamna a karo na biyu, a gidan gwamnatin jihar kano.

Ya ce saboda amincewa da yadda matasa ke kokari wajen ganin an samar da al’umma ta gari, hakan ta sa gwamnatinsa ke kokarin ganin an tallafi tafiya da kuma rayuwar matasan.

“Ina mai tabbatar muku da cewa mun ga irin kokarin da matasanmu na wannan jiha su ka yi lokacin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma zaben gwamna da zabubbukan ‘yan Majalisar Tarayya da na jiha,” in ji shi.

Ya ci gaba da cewa “Kasancewar irin wannan jajircewa da matasanmu su ka yi, ya nuna a fili cewar sun yunkuro sun nunawa duniya cewar lallai za a iya gogayya da su wajen gudanar da shugabanci na gari wanda zai amfani dukkan al’umma. Za mu yi wannan tafiyar da su saboda mu na da tabbacin cewa sun yunkuro saboda su bayar da ta su gudummawar wajen raya kasa da al’umma.”

Gandujen ya kara da cewa, saboda irin namijin kokarin da matasan su la nuna wajen kara samun tabbatuwar zaman lafiya, bayan kammala zabubbukan da a ka kammala kwanan nan, ya zama karin karfafa gwuiwa idan a ka nuna matasan su na da muhimmanci wajen gina kasa.

Wannan maganar ta gwamna Ganduje, kamar yadda shugaban Majalisar Matasan Na Kasa, Bello Bala Shagari ya bayyana, tabbatuwar gagarumar nasara ne da gwamnatin jihar Kano ke son assasa shi a wannan bangare na wannan kasa. Wanda kuma zai iya bazuwa zuwa ga dukkan sasaa na wannan kasa.

Shugaban ya kara da godewa gwamna Ganduje saboda hobbasa da gwamnan ya yi ta yi har sai da a ka samu tabbatuwar samar da shugabancin wannan Majalisar Matasan na farko daga yankin Arewa Maso Yamma na wannan kasa.

Ya kara yabawa Ganduje ganin yadda gwamnan ya rungumi harkokin Majalisar da matukar muhimmanci. “Haka nan kuma Alhamdulillah mun ga yadda Maigirma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya samar da mukamai ga matasa a wannan zubin farkon na mulkinsa,” in ji shi.

Ya kara wata godiyar sabuwa jin cewa ga maganar da gwamnan ya yi wajen kara samar da gurabe ga matasa a juyowa ta biyu ta mulkinsa.

Ya ce “Maigirma gwamna tun ma kafin mu zo wannan waje, mun tabbatarwa da kan mu cewar za mu zo wajen gwamnan da ya dauki matasa da muhimmancin gaske. Alhamdulillah sai ga shi kuwa ka fitar da mu kunya ka tabbatarwa da kowannenmu cewar haka kake.”

Shagarin ya kara yabawa da ayyukan cigaban kasa da gwamnan Kanon yake jajircewa a kai, da yawun Majalisar Matasa ta Kasa din. Ya ce “Wannan Majalisa ta mu ta na mai tabbatar maka da goyon bayanmu kowane lokaci domin samun dorewar wannan mulki cikin nasara da kwanciyar hankali.”

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai Na Gwamnan Jihar Kano

Leave a Reply

%d bloggers like this: