Shahararren Tsohon ɗan wasan kulob ɗin Real Madrid da ke ƙasar Spain,kuma ɗan asalin ƙasar portugal, Cristiano Ronaldo, a shekaranjiya Laraba ne ya fito fili tare da yaba wa kocin ƙungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Zinedine Zidane.
Inda Ya ce a gaskiya Zidane ƙwararren koci ne wanda ya san yadda yake tafiyar da harkar horarwa, wanda hakan ta sa yake samun nasara a hakokin sa na horaswa
Zidane dai ya samu nasarar lashe kofunan zakarun kulob ta nahiyar Turai sau uku a jere amma sai ya yi murabus a farkon kakar wasa ta bana. Daga bisani A watan jiya ya sake karɓar ragamar horar da Madrid bayan mahukuntan ƙungiyar sun lallashe shi.

Ronaldo, wanda ya canza sheƙa zuwa kulob ɗin Juventus dake ƙasar Italiya, kafin ya bar Madrid ya lashe kofin zakarun kulob na Turai sau hudu, sai dai uku daga cikin nasarorin da ya samu, ne a ƙarƙashin horarwar Zidane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: