Duk da cewa shugaban ƙasa Muhhamadu Buhari ya bayyana cewar da batun yake kwana yake tashi amma har yanzu an gaza cimma ɓarnar ƴan bindiga.

A jihar Zamfara da wasu tituna da ke da alaƙa da hanyar ana cikin fargaba ga masu sintiri bisa ɗauki ɗai ɗai da ake a kan hanyar.

Baya ga harin ta addanci da ake kaiwa lungu da saƙo na sassa daban daban na jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.

Ko da a kwanakin nan ma dai an kai mummunan hari inda aka hallaka ƴan ƙungiyar sa kai don daƙile ɓarnar.

Wasu ƴan Zamfaramazauna birnin tarayya Abuja sun yi zanga zanga tare da zargin shugaba Buhari da nuna galin ko in kula a kan kisan gillar da ake yi

Al amarin dai ya sa anata cece kuce muaamman a dandalin sada zumunta inda mutane ke ƙalubalantar gwamnatin da bawa wata ƙabila fifiko bisa dubban mutane da ke rasa rayukansu a Arewacin ƙasar.

Shugaban ƙasa Buhari ya ce shashanci ne ga masu ɗauka cewar ba ya damuwa da halin da mutanen Zamfara ke ciki kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta sanar.

Ko da a titin zuwa Abuja daga Kaduna ma ana samu ƙaruwar masu garkuwa da mutane, wanda ke hallaka wasu bayan sun karɓi maƙudan kuɗaɗe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: