Honarabil Muhaad Aminu Adamu da mutane ke kira Abba Boss ya ce za su bayar da dukkan gudunmawa don ganin talakawa sun amfana da salon mulkin gwamnan Kano da ma shugaba Buhari.

Ya ce matuƙar aka cigaba da tafiya za su nusar da gwamnati kurakuren da ta yi a baya don ganin ta gyara, tare da bijiro da sabbin hanyoyin da talaka zai san ana mulki a juhar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Cikin shirin Abokin Tafiya da mujallar Matashiya ke zantawa da shi duk wata, Abba Boss ya sha alwashin kutsawa don shawartar gwamnatin da nufin gyara kurakurenta na baya.

Ya bayar da misalin mazaɓarsa ta gama, cewar akwai buƙatar ƙarin rijiyar burtsatse don ƙaramar hukumar Nassarawa ta fi kowacce ƙaramar hukuma tsananin ruwan sha a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: