Shugaban ƙasar Najeriya Muhamamdu Buhari ya koka matuƙa kan yadda wasu ke zargin sa da rashin nuna kulawa da damuwa kan halin da jihar Zamfara ke ciki.
Buhari ya ce duk masu yi masa wannan tunani, sun zalinceshi saboda masu zargin basu san irin ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi ba don ganin an kawo ƙarshen wannan matsala.
Shugaban ya bayyana hakan ne a saƙonnin da ya tura a shafinsa na Twitter, a ranar Lahadi.
Inda ya ƙara da cewa, “rashin hankali ne da rashin adalci a riƙa cewa ban damu da halin Zamfara ke ciki ba ko kuma ba na taɓuka komai kan hakan alhali tabbatar da kariya ga al’ummar Najeriya na ɗaya daga cikin manyan nauyin da ke wuyana don haka dole nayi ƙoƙari naga na sauƙe nauyin Al’umma ba ki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: