A yau ne kotun da aka kafa kan sauraren ƙararrakin Zaɓe TRIBUNAL ta jihar kano ta bada Umarni ga hukumar zaɓe mai zaman kanta Reshen jihar kano.
Cewa INEC ta bawa jam’iyar PDP duk wasu bayanai da suka nema Wanda zasu, samu cikakkun hujjojin da zasu gabatar a gaban kotu.

Tun a baya dai Jam’iyar PDP ta Rubutawa Hukumar zaɓe ta ƙasa reshen Jihar kano cewa tana bukatar wasu kayayyakin da aka gudanar da zaben Gwamna dasu domin Samun bayanai dazasu basu damar kammala tattara bayanai da zasu shigar da ƙara gaban kotun sauraren kararrakin zaɓe (Tribunal) ,
Sai dai hukumar zaɓen taƙi yarda ta bawa Jamiyyar PDP wannan bayanai da damar bincika wasu abubuwa Wanda a Qaida duk jamiyyar data rubuta za’a bata damar ganin wannan takardu ko kayyayyakin zaɓe irin su Bayanan Card reader, Ballot paper da aka dangwala, Takardar sakamako da sauransu. A cewar jam’iyar ta PDP.

Hakan yasa lauyoyin jam’iyar ta PDP suka shigar da ƙarar, kan wannan Rashin INEC kan tayi musu Adalci.
Sai gashi a yau kotu ta saurari korafin kuma ta bawa INEC Umarnin ba wa jam’iyar duk wani bayanai da suke nema Wanda zasu samu cikakkun hujjojin da zasu gabatar a gaban kotu, na rashin amincewa da sahihancin zaɓen gwamna da aka gudanar a jihar kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: