Rundunar sojin Najeriya ta daƙile wani hari da ƙungiyar Boko Haram ta nufi kaiwa a Damaturu jihar Yobe.

Rundunar ta ce ta kama muggan makamai da suka haɗa da bindigu ƙirar AK47 da harsashi masu yawa.
Harin dai an yi yunƙurin kaiahi ne a jiya talata da misalin ƙarfe 5 na yamma.

