Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta shaida cewar, tana cikin shirin sabunda doka a kan masu siyar da katin zaɓe.

Shugaban hukumar na ƙasa Farfesa Mahmood Yakub ne ya bayyana hakan yayin wani taro da aka yi a Abuja kan yadda za a magance cin hanci da rashawa.
Ya ce hukumar na shirin gabatar da dokar a gaban majalisa don yin bitarta tare da neman amincewar majalisar.

A cewar shugaban zaɓen, babban ƙalubalen da aka fuskanta a zaɓen bana bai wuce yadda aka ringa cinikin katin zaɓe a lokacin zaɓe ba.

Ya ce za a ɗaure duk wanda aka kama yana siya ko siyar da katin zaɓen shekaru uku cif a gidan yari, ko tarar 500,000 ko kuna a ɗaureshi kuma sannan ya biya tarar.