A dai dai lokacin da aka sasanta Adam Zango da Ali Nuhu wata rigimar ke ƙoƙarin ɓallewa.

Ana zargin wata shahararriyar jarumar fim ɗin hausa da tafka gagarumin alkaba i, ko da dai an shiga don rufa rufa a kan maganar ganin mummunar illar da za ta haifarwa masana antar.
An sasanta tsakanin fitattun jaruman Kannywood guda biyu, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a Kano.

Kwanaki biyu rak suka rage a ahiga kotu don fara sauraron ƙarar da Ali Nuhu ya kai Adam Zango.

Hadaddiyar kungiyar masu shirya finafinan Hausa ta kasa, MOPPAN, karkashin jagorancin Malam Abdullahi Maikano ce ta yi wannan aiki a ofishin dattijon Kannywood kuma shugaban majalisar amintattu na kungiyar, wato Malam Abdulkarim Mohammed a yau Asabar.
Rikicin ya samo asali ne tun bayan zargin cin mutuncin mahaifiyar Adam Zango ya ce yaran Ali Nuhu na yi masa.