Babbar kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Kaduna ta tabbatar da Abba Kabir a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamna a jam iyyar PDP.

Hakan na ƙunshe cikin sanarwar da mai magana da yawun Abba Kabir Sunusi Bature ya raba ga manema labarai.
Mai shari a Tanko Hussaini ya tabbatar da hakan yayin zaman kotun bayan da babbar kotun tarayya da ke Kano da ce Ibrahin Little nw ɗan takarar gwamna a PDP.

Kotun ta tabbatar da cewa babu sunan Ibrahim Little a jerin sunayen ƴan takarar gwamna a PDP.

A cewar mai shari a, kotun jihar Kano ba ta da hurumi gudanar da shari ar.