Ɗan siyasar nan a Jihar Kano Muhammad Aminu Adamu wanda ake kira Abba Boss ya bayyana hanyar da suka bi suka ci zaɓe a Kano.

Abba Biss ya bayyana hakan ne cikin shirin Abokin tafiya da ake tattaunawa da shi a Mujallar Matashiya.

Ya ce a lokacin zaɓen gwamna kafin a tafi zagayen cikon giɓi ƴan kwankwansiyya sun fito da mutane da yawansu ma a a hayyacinsu suke ba, hakan ya sa mutanensu shiga shakku wajen bayyana a wajen zaɓen.

Cikin shirin ya bayyana nasararsu da ɗaukar matakin kowa kwamanda ta hanyar zuba dakarunsu don tsare akwatunansu.

Ya ƙara da cewa duk jita jitar da ake yaɗawa cewa an yi riguma a Gama, a cewarsa ko mutum ɗaya bai ga an nunawa yatsa ba.

Abba Boss ya alaƙanta rashin nasarar jam iyyar PDP da hanyar da suka bi wajen zaɓen ƴan takara.

Sannan ya sha alwashin cigaba da ƙoƙari wajen kawowa al ummar jihar Kano ayyukan cigaba ta hanyar miƙa ƙoƙon bararsu ga gwamnan jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: