Connect with us

Rabin ilimi

Ya halatta a raƙashe yayin biki kafin ɗaura aure

Published

on

Wata ta aiko da tambaya cikin shirin rabin ilimi da mujallar Matashiya ke gabatarwa cewa menene hukuncin yin biki wanda ya haɗar da Party, Dinner, Kanu kafin ɗaura aure.

Mallam Muhammad Tukur Moriki ya ce matuƙar al’ada ta zo kuma ba ta yi karo da addini ba, babu laifi yin hakan kafin biki ko bayan biki.

Sai dai abin dubawar shi ne, me ake yi idan an ce wajen? To wannan wajibi a faɗa haramun ne idan ya haramta in kuma babu laifi to babu makawa za a iya yin bukukuwa kafin ɗaura aure da kuma bayan an ɗaura aure.

Click to comment

Leave a Reply

Rabin ilimi

Duk wasan Hausa ko waƙar da ba zai taimaki musulunci da musulmi ba haramun ne – Shek Moriki

Published

on

Wasan Hausa da waƙar da za su taimaki musulunci da musulmi ne kaɗai ya halatta ba shiririta ba, Duk waƙa ko wasan Hausar da ba zai taimaki musulunci da musulmi ba haramun ne inji shek Moriki

Babban malami a Hukumar Hizba ya jaddada fatawar da ya bayar na cewa ya halatta a yi wasan Hausa da waƙar da za su taimaki addinin musulunci da musulmi.

Malamin da wasu ke ɓatanci a kansa bisa fatawar da ya bayar, ya barranta kansa da cewa wasu ɓata gari ke masa ɓatanci wasu kuwa akasin fahimta ne.

Shek Moriki ya bayar da fatawar ne cikin wani shiri da ake gabatarwa na Rabin Ilimi a Mujallar Matashiya.

Wanda daga baya wasu ke sukar fatawar, malamin ya ce muddin aka yi wasan Hausa ko waƙar da ta saɓawa addini to haramun ne aikatata ƙarara musamman abinda zai rusa tarbiyya.

Continue Reading

Addini

Rabin Ilimi – Zan iya biyawa kaina buƙata da hannu saboda tsananin sha awa? –

Published

on

Da yawan mutane na fama da tsananin sha awa sai dai wasu na rasa yadda za su saka kansu.

A wasu lokutan wasu kan yi amfani da hannunsu wajen biyawa kansu buƙata, kamar yadda wata ta aiko da tambaya ta cikin shirin da muke amsa tambayoyin da kuke aiko mana a bisa tafiyar rayuwar addinin musulunci.

Wata baiwar Allah ta aiko da tambayar cewa za ta iya biyawa kanta buƙata da hannunta saboda tsananin sha awa?

Shek Muhammad Tukur Moriki ne ke amsa tambayar ya kuma ce, biyawa kai buƙata da hannu tamkar mutum ya aikata zina ne.

Kuma duk mutumin da ya kasance mai auren hannunsa Allah S.W.A ya tsine masa, sai in har ya tuba daga aikata hakan.

Malam Moriki ya ce akwai hanyoyi da mutum zai iya katange kansa, misalin yin azumi, da kuma kaucewa kallon abinnda zai tada hankali izuwa sha awa.

Continue Reading

Rabin ilimi

Saboda tsananin soyayya ta sa ya fara runguma ta

Published

on

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: