TRAN VAN HAY ya kasance dan asalin kasar Sin wato China, kuma shi ne mutumin da yafi kowa tsawon gashin kai a duniya, ya kasance yana yin gammo da gashin kansa, wanda kuma ya bayyana cewa sam baya jin nauyin gashin kan nasa idan yana tafiya.

Tran duk day a kwashi tsawon shekaru a duniya amma yakan jure dakon gashin kan nasa, idan ya nada gashin a kansa kai kace wani duro ya dakko.

Tran wanda yace tsawon gashin kan nasa ya samo asali ne tun yana dan shekara ashirin da biyar, yayin da yake kuruciya, ya fara barin gashin kan nasa a matsayin ado, kamar yadda ya bayyana, tun a wancen lokaci ya fara barin gashin kan nasa.

Tsawon gashin kan Tran dai ya fishi tsayi,  wanda ko da tsayawa yayi a tsaye sai ya nade gashin da hannu musamman ma idan zai yi tafioyar kasa,.

Shekaru kusan hamsin ya kwashe yana barin gashin kansa wanda kuma ya bayyana farin cikinsa a bisa kasancewa da yayi na daya a wadanda sukafi tsawon gashin kai a duniya.

Tran ya bayyanawa yan jaridu cewa kwata kwata bashi das ha awar aske gashin kan nasa, musamman idan aka yi duba ga irin shekarun day a kwashe yana tara gashin.

Tsawon gashin tran dai ya kasance babban inci 26, idan masu karatu ba ku manta ba mujallar Matashiya ta kasance tana kawo muku labaran al ajabi musamman wadanda suka sha bam bam a  duniya

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: