Labaran ƙetare
Wanda ya fi kowa gashin kai a Duniya
TRAN VAN HAY ya kasance dan asalin kasar Sin wato China, kuma shi ne mutumin da yafi kowa tsawon gashin kai a duniya, ya kasance yana yin gammo da gashin kansa, wanda kuma ya bayyana cewa sam baya jin nauyin gashin kan nasa idan yana tafiya.
Tran duk day a kwashi tsawon shekaru a duniya amma yakan jure dakon gashin kan nasa, idan ya nada gashin a kansa kai kace wani duro ya dakko.
Tran wanda yace tsawon gashin kan nasa ya samo asali ne tun yana dan shekara ashirin da biyar, yayin da yake kuruciya, ya fara barin gashin kan nasa a matsayin ado, kamar yadda ya bayyana, tun a wancen lokaci ya fara barin gashin kan nasa.
Tsawon gashin kan Tran dai ya fishi tsayi, wanda ko da tsayawa yayi a tsaye sai ya nade gashin da hannu musamman ma idan zai yi tafioyar kasa,.
Shekaru kusan hamsin ya kwashe yana barin gashin kansa wanda kuma ya bayyana farin cikinsa a bisa kasancewa da yayi na daya a wadanda sukafi tsawon gashin kai a duniya.
Tran ya bayyanawa yan jaridu cewa kwata kwata bashi das ha awar aske gashin kan nasa, musamman idan aka yi duba ga irin shekarun day a kwashe yana tara gashin.
Tsawon gashin tran dai ya kasance babban inci 26, idan masu karatu ba ku manta ba mujallar Matashiya ta kasance tana kawo muku labaran al ajabi musamman wadanda suka sha bam bam a duniya
Labaran ƙetare
Trump Ya Zabe Wanda Zai Masa Mataimaki
Dan takara shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zabi Sanata J.D Vance a matsayin wanda zai masa mataimaki.
Sanata J.D Vance dai na da shekaru 39 a duniya wanda a baya ya kasance mai caccaka da sukar tsarin siyasar Donald Trump.
Sai dai daga baya ya dawo goya masa baya.
Donal Trump na takarar shugaban kasar Amurka ne karkashin jam’iyyar Republican.
A makon jiya ne aka kai hari Pennsylvania yayin da yake gangamin yakin neman zabe.
An bude wuta a wajen sai dai daga baya jami’an tsaro sun kubutar da shi duk da cewar ya ji rauni a fuskarsa da kunnensa.
Donal Trump ya ce an so a hallakashi ne a wajen taron amma Allah ya tseratar da shi.
Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya yi Ala Wadai da lamarin.
Ya bukaci yan kasar da su hada kai don tabbatar da zaman lafiya.
Ana sa ran za a yi zaben ne a watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki.
Labaran ƙetare
Ya Kamata A Dinga Jefe Ƴan Luwaɗi Da Maɗigo – Shugaban Ƙasar Burundi
Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya bayyana matakin da ya kamata a rinka dauka kan masu neman maza waɗanda aka fi sani da ‘yan luwadi.
Evariste ya ce kamata ya yi a rinka jefe su da su da masu auren jinsi inda ya ce hakan ba wani laifi ba ne.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba.
Ya ce kasarsa ba ta bukatar duk wani taimako daga kasashen Yamma a kokarin kakaba musu sharadin luwadi da madigo.
Har ila yau, shugaban ya ja aya a cikin littafin Inijla inda ya ce Ubagiji ya haramta neman jinsi kwata-kwata.
Ndayashimiye ya kara da cewa kasarsa bata bukatar fara tattauna magana kan ‘yan luwadi da masu auren jinsi.
Ya ce luwadi da madigo hanya ce a bayyane tsakanin hanyar gaskiya ta ubangiji da kuma hanyar bata ta shaidan.
Burundi na daga cikin kasashen Afirka da suka haramta luwadi wanda hakan ya sa aka sanya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
Labaran ƙetare
Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu
Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.
Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.
Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.
Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.
Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.
Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari