NICK STOEBERL

Ya kasance mutumin da ya fi kowa tsawon harshe a duniya, wanda duniya ta tabbatar da hakan.
Nick ɗan asalin ƙasar amurka ya bayyana farin cikinsa da yake ciki a yanzu kasancewar duniya ta nunashi a matsayin wanda yafi tsawon harshe a duniya, “dun da kasancewar a lokacin yarintata abokaina yara sun kasance suna tsokanata wanda hakan sam bana jin daɗinsa, amma daga ƙrshe na kasance mai alfahari da ƙatoton harshena” inji Nick.


Ya ce ya fuskanci ƙalubale musamman idan ya nuna wata a matsayin wadda yake so wato budurwarsa sai su rionga gudunsa suna ɗaukarsa kamar wani daban ba jinsin mutane ba, amma hakan bai sa ya gajiya ba.
Hatta ƙawayensa ko da a makaranta ba su cika hulɗa da shi ba sanadin ƙaton harshensa wasu ma sukan kirasa da maye amma a matakin da yake a yanzu mutane da dama na rububin ganinsa, wasu ma na so yayi abota ko ƙawance da su amma saboda tsabagen yawan jama ar da yake da su ba zai samu damar yin mu amala da kowa ba.
A yanzu dai mista Nick ya karɓi kyautuka da dama a matsayin wanda duniya ta tabbatar da cewa ya fi kowa tsawon harshe a duniya, kuma yakan yi mu amala da kowa saɓanin a da wanda mutane ke gudunsa.