
Uwar gida da amarya barkanmu da wannan lokaci, sannunmu da sake haɗuwa ta cikin shafin girke-girke a yau za mu kawo yadda ake sarrafa lemon shinkafa.


Kayan haɗin da ake buƙata sune kamar haka:-
Danyer Shinkafa
Dankalin Hausa
Sugar
Flavour
sai kuma Citta da kanumfari.
Yadda za a hada shi
Idan kika sami dankalinki na Hausa, bayan kin fere shi sai ki sami danyar shinkafarki ita ma bayan kin jika ta ta jiƙu, sannan sai ki sa ‘yar Cittarki da dan kanunfari shi ma sai ki zuba kadan. Sannan sai ki kawo Wannan danyan dankalin wanda kika fare shi sannan kika yayyanka shi kanana sai ki markade Sai ki hada a cikin jikakkiyar shinkafarki sai ki hada ki markade. Bayan kin tace da rariya mai laushi,sai ki kawo sugarki wanda daman na rigaya na gaya miki ana so ki dafa shi sai ki zuba daidai yadda kike so.Sannan sai ki zuba flavour a ciki sai ki sanya ya yi sanyi.
Da fatan za gwada don jin daɗin da yake ɗauke da shi, mu saɗu a wani watan don karanta wani sabon girki na zamani da za mu kawo muku.