Maimuna Umar Sharif lauya ce da ke bibiyar haƙƙin waɗanda aka zalinta musamman a fanni na fyaɗe.

Kamar yadda kuka sani dai mafi yawancin lokuta akan samu yawaitar fyade wanda daga bisani kuma da zarar an yanke hukunci ba sa kai shekarun da aka yanke sai mutum ya dawo a sakeshi.
Lauya ta ce a ƙoƙarinsu na ganin an magance matsalar baki ɗaya suna ƙoƙari don ganin an ƙara wa adin zaman gidan kaso ga duk wanda aka tabbatar da ya aikata laifin, daga shekara 14 zuwa shekara 25 domin na baya su hankalta tare da gujewa aikata hakan.

Haka kuma ta yi kira ga masu ƙoƙarin fitar da waɗanda suka aikata laifin da su gane cewa hakan da suke ba dai dai bane domin bari a hukunta mai laifi shi ne adalci ga wadda aka yiwa laifin.

Kafin shiga cikin shirin ta yi waiwaye a shirin ina mafita da ya gabata wanda ta bayyana cewa babu hujjar da kotu za ta hukunta Maryam sanda, wato wannan baiwar Allah da ake zargi da hallaka mijinta a babban birnin tarayya Abuja wadda ta ce hakan ba ra ayinta bane sannan ba ta karbi kuɗi don karesu ba aa doka ce ta zo da hakan.
Za ku iya kallon shirin a shafinmu na youtube wato mujallar Matashiya.