A ranar laraba 24/4/2019, mai girma kwamishinan yansanda na jihar Kano, CP Wakili Mohammed FSI ya fara kai ziyarar gani da ido a ofishin yankuna na Yansanda da ke Kano, inda ya fara da zuwa yankin Metro, Dala da kuma yankin Kano ta tsakiya.

Haka kuma a ranar Alhamis 25/4/2019, Mai girma Kwamishinan Yansanda na jihar Kano CP Wakili Mohammed fsi ya kai ziyara yankin Hotoro, Tarauni da kuma Eastern bye-pass, a yayin ziyarar Kwamishinan ya gana da dunbin mutane kama daga Yan Kasuwa, Malamai, masu sana’ar hannu, kungiyoyi, shugabannin al’umma da kuma jami’an Yansanda, sannan ya yi kira ga jama’a da su cigaba da ba wannan runduna goyon baya da hadin kai don tabbatar da cikakken tsaron lafiya da dukiya. Jama’a sun jinjinawa mai girma kwamishinan bisa jajircewarsa a kan aiki, kuma suka bashi kyaututtuka daban-daban.

Allah ya taimaka ya kuma bamu zaman lafiya mai dorewa a Kano.

Duba Hotuna a Kasa:

Leave a Reply

%d bloggers like this: